GABATARWA
Assalamu alaikum dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ALLAH,tsira da aminci su tabbata ga annabi MUHAMMAD s.a.w.bayan haka ina mai farincikin saduwa daku a wannan shiri mai taken html tutorial wanda ni cyberibrahim zan rinqa gabatarwa da yardar ALLAH.yau zamu fara da gabatarwa.dafarko kalmar html tana nufin hypertext markup language,wanda shine building block na shafin yanar gizo,kamar yanda muka sani a k-mis-3 atoms sune abubuwan da suke haduwa su bada matter,to shi ma haka html code su suke haduwa su bada webpage SAUQAQAQQEN MISALIN HTML
.
.
.
<!DOCTYPE html>
<html>
<head>
<title> www.hausanet.com
shafin koyan kimiya,labarai dss
</title>
</head>
<body>
<h1>menene ma'anar html?
</h1>
<p>
sakin layi na farko
</p>
</body>
</html>
.
.
.
.
bayanin misali
-shi <!DOCTYPE html> alama ce da take nunawa na'urar lilo cewa za a rubuta html code.
-shi kuma <html> element ne dake nuna inda aka fara ko kuma tushen html code.
-shi kuma <head> element ne da suke acikin meta,su bawai a shafin zakagansu ba,ana ganinsu ne daga can samanshafi,ana anfani dasu ne wajen searching ta search engines.
-shi kuma <title> yana nufin sunan shafi.
-shi kuma <body>sune wuraren da ake gani a screan,misali a homepage na wasu shafukan akwai login,registration dss.
-shi kuma <h1> element ne da yake nuna babbar maudu'i,ma'ana heading kenan a turance.
-sai na karshe wato <p>wanda shi kuma yana nuni ne akan paragraph...
skilled by ibrahim.
ALAQAR HTML DA CSS
html yana nufin gimshikin shafin yanar gizo,xaka iya kiransa blocks na html kamar yanda shi kuma css shine yake karawata html.misali idan ka gini to kayi html amma a lokacin da kake plaster da penti css kakeyi.
kamar yanda na fada a darasi na farko,kalmar html shortcut ne na hypertext markup language,masana da yawa sunyi ittifaqin cewa html markup language ne ba programming language ba.
mu hadu a darasi nagaba
ka qiyasta,kafin a kirkiro yanar gizo,babu shafunkan websites da blogs,amma a yanxu kana da damar bude kowacce kalar browser dakai raayi kai bincike aken abun dakaga dama,insha Allah zanyi kokari a wannan shiri namu naga mun fahimci me ake nufi da html sosai.kuma naga na samar maku da hanyoyi masu sauki na hada websites da blogs.
akwai yaruka guda uku zuwa hudu wanda ake hada shafukan yanar gizo.
1.HTML
2.CSS
3.JAVASCRIPT(JS)
4.PHP.
kafun mu tsunduma cikin darasi,ya kamata musan anfanin wadannan yaruka.
mu hadu a darasi na uku
HTML TAGS.
skilled by ibrahim.
.
.
.
html tags sunayen element ne,dake kasancewa tsakanin angle bracket guda biyu.
.
.
.
<sunan tag>
rubutu anan
</sunan tag>
html tags kala biyu ne xuwa uku.
skilled by ibrahim.
1.openin tag(ko start tag)
2.closing tag(ko end tag)
3.self closing.
-opening tag:shine wanda yake zuwa a farko,misali <i>,<p>,<u>,<blink>,<b> dasauransu.
-closing tag:shine wanda yake zuwa a qarshe,banbanshi da opening tag alama daya ce,slash(/).
-self closing:wannan shine wanda ba dole sai kasa masa closing tag ba,kamarsu <br> dasauransu.
skilled by ibrahim